27 Satumba 2020 - 11:40
Habasha Ta Ce; Ba Ta Da Niyyar Cutar Da Kasashen Masar Da Sudan Akan Madatsar Ruwan Da Ta Gina

Fira ministan na kasar Habasah Abiy Ahmed ya bayyana cewa; “ Ina son tabbatar da cewa muna akan aniyarmu ta warware rashin fahimtar wadannan kasashen da kuma cimma matsaya akan yadda dukkanin bangarorin za su amfana a karkashin jagorancin kungiyar tarayyar Afirka.”

ABNA24 : Kasar Masar dai ta yi gargadin cewa gina madatsar ruwan za ta iya yin mummunan tasiri ga tattalin arzikinta, saboda yadda kwararowar ruwan maliya zai ragu matuka.

Bugu da kari Masar din za ta sami koma baya matuka dangane da ruwan shan da take samu da kuma albarkatun kifi da ma ruwan noma rani da kaso mai yawa.

Fira ministan kasar ta Habasha ya bayyana hakan ne a jawabin da ya yi wa babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ta hanyar watan Bidiyo daga nesa.

342/